Wadanne Ƙasashe Ne Ke Ci Gaba Da Aika Makamai Zuwa Isra'ila Duk Da Amincewarsu Ga Ƙasar Falasdinu?

Spain Ta Soke Yarjejeniyar Cinikayyar Makamai Karo Na Uku Da Isra'ila
26 Satumba 2025 - 15:47
Source: ABNA24
Wadanne Ƙasashe Ne Ke Ci Gaba Da Aika Makamai Zuwa Isra'ila Duk Da Amincewarsu Ga Ƙasar Falasdinu?

Daga cikin kasashen da suka amince da Falasdinu, wasu kamar Belgium, Spain, Norway, sun kakabawa Isra'ila takunkumin soji da na tattalin arziki; amma kasashen Faransa, Britaniya, Canada, da Ostireliya na ci gaba da aikewa da makamai da kayan yaki zuwa Isra'ila.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Duk da martanin da Netanyahu ya yi na kin amincewa da kafa wata kasar Falasdinu wasu ƙasashen duniya Musamman ma, Biritaniya da suka amince da kafa kasar Falasdinun ta aike da dubban makamai masu linzami, tankunan yaki, bama-bamai, gurneti, da bindigogi zuwa Isra'ila a cikin shekarar da ta gabata, baya ga samar da sassan jirgin yaki nau'in F-35. Kanada ta kuma aike da kayan yaki da yawa zuwa Isra'ila, da suka hada harsashai 400,000 da kuma sassan jiragen soji, a daidai wannan lokacin. Kasar Faransa ta kuma mikawa Isra'ila bama-bamai miliyan 15, gurneti, makamai masu linzami, harsasai, da bindigogi ga Isra'ila, baya ga karfafa tsarin makami mai linzami na Iron Dome.

Spain anata martani ta soke yarjejeniyar cinikayyar makamai karo na uku da Isra'ila.

Wadanne Ƙasashe Ne Ke Ci Gaba Da Aika Makamai Zuwa Isra'ila Duk Da Amincewarsu Ga Ƙasar Falasdinu?

Yayin da ake ci gaba da samun karuwar hare-haren da sojojin Isra'ila ke kaiwa Gaza, gwamnatin Spain ta soke yarjejeniyar sayen makamai da ta kulla karo na uku, kwanaki biyu bayan da dokar hana cinikin makamai da Isra'ila ta fara aiki.

Jaridar Haaretz ta Isra'ila a yau ta bayar da rahoton cewa, yayin da ake ci gaba da gwabza yaki a Gaza, Spain ta soke yarjejeniyar sayen makamai da ta kulla da Isra'ila, wanda ya kai tsabar kuɗin Euro miliyan 207, kwanaki biyu bayan da dokar hana cinikin makamai da Isra'ila ta fara aiki.

Your Comment

You are replying to: .
captcha